Injiniya Dakta Muhammad Kabir Abdullahi ya kaddamar da bude sashin koyan sana'a a makarantar Demonstration dake Zaria

Ishaq Umar Abbas


Shugaban kwalejin kimiyya da fasaha ta Nuhu Bamalli da ke Zariya, Injiniya dakta Muhammad Kabir Abdullahi ya kaddamar da bude sashin koyan sana'a da ya kunshi wurin dinkin kaya da gyaran gashin mata a makaranta Demonstration dake Zaria. 
Kaddamarwar, wacce ta gudana jiya a harabar makarantar, ta sami halattar wasu malamai da daliban makarantar. 


A lokacin da Injiya Muhammad Kabir ke zan tawa da gidan radiyon Nubapolyfm, ya nuna jin dadin shi tare da jinjina ma mahukunta makarantar baki daya,  gamin yadda tun farko suka kawo shawarar wannan aiki, tare da tabbatar da an aiwatar da aikin yadda ya kamata. 
Dakta Kabir ya jawo hankalin dalibai da su maida hankali wurin cin moriyar wannan fanni na sana'ar hannu. 
Shima shugaban kwamitin gudanarwa na makarntar demonatration, wato Dakta Adamu Ishaq Kauru, yace shrin koyar da sana'ar an gwamashi cikin tsarin karatun dalibai, wato time table, yadda komai zai tafi kamar sauran darussa. Ya kara da cewa, nan gaba suna sa ran shigo da sauran makarantu na kusa don suma suci ga jiyar wadannan sana'o'i. 


A ta bakin shugaban cibiyar koyar da sana''oin, Mallam Bala Galadima, yayi godiya ga sauran malamai da suka taimaka wurin cin ma wannan buri.Sannan ya kara da cewa wadannan bangarorin sana'o'i na dinki da gyaran gashi kari ne akan bangarorin koyar da aikin katakai(wood work) da kuma latoroni(electronics), da dalibai na manyan sakandire keyi. 
A wani bangaren kuwa, Mallam Umar mai koyar da harshen turanci a makarantar, ya ayyana cewa wannan makaranta itace ta fara bude irin wannan sashi na koyar da sana'o'i a Zaria ko ma jihar kaduna baki daya. 
Itama Mallama Na'ima wacce bangaren gyaran gashin mata ke karkashin ta, ta nuna shirin ta don bama dalibai duk abinda ya kamata don dogaro da kan su a nan gaba. 

Da Nubapolyfm ta waiwaya kan dalibai kuwa, shugaban dalibai maza Abubakar Ibrahim Abubakar, da takwararsa na mata Rukayyah Mukhtar, sun nuna farin cikin su da wannan wurin yazo kafin su gama makaranta, sun kuma ja hankalin 'yan uwan su dalibai wurin ganin sun cin gajiyar wannan bangare don samun madogara nan gaba, ganin yadda aikin gwamnati ke wuya a halin yanzu. 
Nubapolyfm ta sami damar ganin wasu aikace-aikace da daliban koyan aikin katakai sukayi na tebura da walda. 
1 Comments

Post a Comment