Ƙungiyar Ƙwallon Kafa Ta Manchester City Zata Cigaba Da Bibbiyan Cin Ƙofin Carabao Karo Na Biyar

Aliyu Umar
Ƙungiyar Ƙwallon Kafa Ta Manchester City Zata Cigaba Da Bibbiyan Cin Ƙofin Carabao Karo Na Biyar, Wanda Ta Samu Nasarar Lashe Ta Har Na Tsohon Shekara Hudu(4) A Jere, Yayin Da Zata Papata Da Abokiyar Hamayyar Ta Me taƙen Westham. 

Bayan Nasara Da Manchester City Ta samu Aƙan Kungiyar Wycombe A Wasan Daya Gabata Ranar Talata, Kungiyar Zata Goga da Kungiyar Westham United A Wasan Zagayen Sha Shidan Karshen Na Gasar Kofin Carabao, Bayan Nasaran Da Kungiyar Ta Samu Akan Kungiyar Mancheater United A Ranar Laraba A Gidan Ta, Old Trafford. 

Lashe Kofin Carabao Sau Hudu A Jere Na Nufin Cewa,Kusan Shekara Biyar Kenan Rabon Da A Samu Wadanda Zasu Dakile Masu Nasaran Su. Kungiyar Data Samu Nasaran Lashe Kofin Carabao Na Ƙarshe Kafin Manchester City Ta Fara Kafa Tarihi Sune Manchester United, Yayin Da Suka Lallasa Ma Southampton ci Uku Da Biyu(3-2) A Wasan Ƙarshe na Gasar, Wacce Ta Basu Nasarar Daukan Kofin A Shekara Ta Dubu Biyu Da Goma Sha Shida(2016). 

Kungiyar Manchester Citu Ta Maida Kofin Carabao Tamkar Tasu Tun Zuwan Mai Horas Wan Su Pep Guardiola. Ƙungiyar har Ila Yau Bata Rasa Wasa Ko Daya Ba A Gasar Tun Sanda Babbar Abokiyar Hamayyan Ta Manchester United, Ta Samu Nasaran Lallasa Su A Zagaye Na Hudu A Sheƙara Ta Dubu Biyu Da Goma Sha Shida(2016). 

Post a Comment (0)