BRAZIL TA KIRA 'YAN WASA TAKWAS NA PREMIER LEAGUE DON BUGA WASAR GASAR NEMAN SHIGA KOFIN DUNIYA.

ALIYU UMAR
Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta ƙasar Brazil ta zaɓa yan'wasa Takwas(8)a premier league da zasu buga gasar neman shiga ƙofin duniya(World Cup), na watan oktober, ɗuƙ da ƙasar na ciƙin jerin sunayen kasashen da Ingila ta hana shiga saboda cutar korona. 

Yan wasa takwas din sun hada da Yan'wasan liverpool, Alisson da Fabinho, tare da Ederson da Gaberial Jesus na Manchesterb city , da dan wasan baya na Chelsea Thiago Silva, da na tsakiyan manchester united, Fred da Rapinha na leeds da Emerson Royal na tottenham., duk suna cikin wadanda aka kira dan buga wasanni tsakanin Brazil da Venezuela, Columbia da Uruguay. 

Kungiyar tarayyan kwallon kafa na Brazil(CBF) na daya daga cikin kungiyan kasasshe hudu(4)da suka bukaci kungiyar kwallon kafa ta duniya(FIFA) da, ta ajiye yan wasa daga aiyukan kungiya biyar(5). Amma kungiyar tayi watsi da rokon su a ranar Goma(10)ga watar satumba. 

Watan daya gabata, Mafi yawancin 'yan wasa masu buga ma kungiyoyi a Ingila, an ki yarda da sakin su da Kasasshen kudancin Amurka ta kira. A halin yanzu, duk wanda yayi tafiya zuwa Brazil daga Ingila se an killace shi na kwana Goma sha hudu (14), idan suka isa kasar, da kuma kwana Goma(10) idan suka dawo Ingila(U. K). 

Post a Comment (0)