Rikicin kabilanci ya yi sanadiyar mutuwar mutun 10 a jihar Benue

Daga Sani Umar 

Sama da mutane goma aka kashe a wani sabon rikici tsakanin kabilar Ezza da Effiuma a iyakar kauyen Karamar hukumar Ado na jihar Benue, da kauyen Ohaukwu dake karamar hukumar Ohaukwu na Jahar Ibonyi. 

Jaridar Daily Post ta Bayyana  cewa, kabilun biyu sun koma yin karo da juna ne, a ranan Juma'ar da ta gabata, wanda ya yi sanadiyar mutuwar a kalla Mutun goma, tare da raunata Mutane da yawa. 

Shugaban Karamar hukumar Ado, James Oche wanda ya tabbatar wa da manema Labarai faruwan lamarin a Makurdi, ya ce, ya roki kabilun biyu da suyi sulhu da juna, kuma su zauna lafiya. 

Duk da haka, Jaridar Daily Post ta tuntubi jami'in hulda da Jama'a na 'Yan Sanda DSP Anene Catherine Suwuese ta shaida da cewa, rundunar batasami rahotan afkuwar lamarin ba.
Post a Comment (0)