Cibiyar wayar da kan yara mata kan mahimmancin Ilimi ta ziyarci Sarkin Zazzau

Abdul'aziz  Idris.


Cibiyar wayar da kan mata kan mahimmancin Ilimi wato, Center For Girls Education a turance, ta gana da Mai-girma Sarkin Zazzau Ambassador Ahmed Nuhu Bamalli a yau Alhamis, a fadar shi da ke birnin Zaria.

A dai yau Alhamis 24 ga watan Yunin shekarar 2021, cibiyar ta  jagoranci mata zuwa ziyara ga saraku nan gari, Malaman addinai, da Dattawan anguwa, ciki harda Sarkin Zazzau, Ambassador Ahmed Nuhu Bamalli, a kan hanyoyin da za’abi, domin zakulo mata masu hazaka, don basu ilimi kyauta,  a yunkirin ganin cibiyar ta cika, daya daga cikin kudurorin ta.

Cibiyar ta ce, wannan ne karo na farko da ta kai wa masarautar Zazzau ziyara cikin ikon Allah, inda ta kara da cewa, sun karu matuka, na yadda manyan mutane, su ka basu shawarwari wajan habbaka wannan aikin alherin da su ke yi, na cire mata daga cikin rashin ilimi, ta cikin shirin su, na ganin sun zakulo mata masu hazaka.

Sun kara da cewa zasuyi amfani da wannan shawarwari, wajan habbaka aiyukan su, na  taimakawa wurin tabbatar da mata sun sami Ilimi ingantacce. 

Inda a karshe cibiyar ta ce, za ta kara dagewa wajan inganta lamuran ta, domin kai wa ga ci.
Post a Comment (0)